Na kamu da cutar tsananin damuwa bayan rabuwa da matata - Zango

hhh
0
 Fitaccen jarumi a masana'antar shirya fina-fina ta Kannywood Adam Zango ya ce ya shiga tsananin damuwa, sakamakon abubuwan da suka taso bayan rabuwarsu da matarsa.

 Cikin tattaunawarsa da BBC a shirin Mahangar Zamani, jarumin ya ce yanzu haka ya ja baya daga harkokin yau da kullum kuma yana nazari domin gano daga ina matsalar take. ''Har yanzu ba mu sasanta da matata ba, hasalima yanzu haka ta kusa yin aure'', in ji jarumin.

 Sai da jarumin ya ce maganar da ya yi a baya cewa ba zai sake yin aure ba, ya faÉ—e ta ne a lokacin da yake cikin fushi, amma yanzu da ya sauko, ya jingine wannan maganar. ''Dole ne na yi aure don kare mutuncin kaina, da na 'ya'yana da kuma na mahaifiyata, saboda a yanzu ne nake cika cikakken mutum'', in ji Adam Zango. Adam Zango ya ce babban abin da ya haÉ—a shi da matarsa da ya saki a baya-bayan nan shi ne amfani da shafukan sada zumunta, wanda shi kuma ba ya so. 
Ya ce a karon farko shi ne ya amince ta riƙa amfani da shafukan domin harkokin kasuwancinta, amma ya ce daga baya sai wasu abubuwa suka riƙa faruwa wanda shi kuma yake ganin ba daidai ba ne. Jarumin ya ce nan gaba idan zai yi aure abin da zai yi la'akari da shi ne danginta, saboda ya ce yawan auren da ya yi ya sa ya gano cewa ana auren mace ne tare da danginta. Adam Zango ya ce babau maganar da ta fi tsaya masa a rai ko take ɓata masa rai ba, irin yadda ake jifansa da siffar mai auri-saki. Jarumin ya ce babban burinsa a yanzu bai wuce samun mace tagari ba.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)