A cikin takardar masu shigar da ƙaran sun yi nuni da cewa ba su gamsu da haƙurin farko da Sadiya Marshal ta bayar ba. Ya zama wajibi a gare ta yanzu ta fito ta ƙaryata kanta ta kuma nemi gafara. Sun ƙara da cewa Onarabul Adamu Gagdi ɗan siyasa ne kana kuma shugaban al’umma mai daraja wanda yake wakiltar garuruwan Pankshim/Kanam/Kanke na Jihar Filato a majalissar tarayya. Yayin da a gefe guda kuma, Hajiya Laylah Ali Othman ke zaman babbar mace mai daraja kana hamshaƙiyar ƴar kasuwa da ke zaman mamallakiyar katafaren gidan abinci na (L&N Kitchen) da katafariyar masana’antar ƙera kayayyakin ɗaki ta (L&N Interios/Furniture) da sauran nau’ikan kasuwanci daban-daban a ciki da wajen Abuja.
Sannan kuma tana da ɗumbin abokan hulɗar kasuwanci (kwastomomi) ɗaiɗaikun mutane har ma da kamfanoni da sauran hukumomi da ma’aikatu. Amma duk da haka Sadiya Marshall ta fito fili ta hau kan manhajar (Facebook) tayi Bidiyo a ranar 27 ga watan 1 na shekarar 2024 ta keta alfarmarsu ta yi maganganun cin zarafi da ɓata musu suna a gaban mabiyansu da kwastomominsu da ma sauran al’umma gabaɗaya wanda hakan zubar musu da mutunci ne tayadda za ta haifar musu da matsala a harkokinsu na siyasa da harkokinsu na kasuwanci.
Jerin laifuffukan da masu shigar da ƙaran suke tuhumar Sadiya Marshall a kai tare da neman ta fito ta janye kalamanta ta kuma nemi gafara ko su haɗu da ita a gaban ƙuliya manta sabo sun haɗa da: